Babban ma shawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, ya hannunta mutane 16 da aka kubutar daga hannun masu garkuwa da mutane ga wakilan gwamnatin jihar Zamfara.
wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da shugaban sashen sadarwa da dabaru na cibiyar yaki da ýan ta’adda a ofishin mai babban mai shawarcin , NCTC – ONSA, a ranar alhamis a birnin tarayya Abuja.
Read Also:
Ribadu yace damka wadanda aka kubutar din na shaida kan yunkurin gwamnatin tarayya kan mabanbanta ceto wadanda masu garkuwa da mutane suka kama sannan ya nuna kokarin gwamnatin tarayyar Nijeriya na kare rayukan ýan Nijeriya da wadanda ke tsare a hannun masu garkuwa da mutane.
Yace an yi garkuwa da mutanen ne a kwaryar Zurmi, Duran da Gusau dake cikin garin Zamfara a ranar 22 ga watan Afrilu, wanda kuma atisayen da NCTC ya sami nasarar kubutar da su.
Ya bukaci al’umma Nijeirya da su cigaba da bawa jamián tsaro goyan baya domin cimma kudirin gwamnatin tarayya na kawar matsalolin tsaro a Nijeriya.
daga bisani kodinatan NTCT, Manjo Janar Adamu Laka ya bukaci al’umma dasu ke gaggauta sanar da Jami’an tsaro da zarar wani lamarin tsaro ya auku domin daukar mataki da wuri.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 13 hours 57 minutes 18 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 15 hours 38 minutes 43 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com