Sojojin saman Nijeriya dake karkashin Operation Hadin kai sun sami nasarar hallaka ýan Ta’adda 7 a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.
wanna na cikin wata sanrwa da darakta yada labarai da hulda da jama’a na rundunar AVM Edward Gabkwet ya fitar ranar alhamisa a birnin tarayya Abuja.
Read Also:
Gabkwet ta cikin sanarwar yace dakarun sun sami nasarar ne bayan farwa maboyar ‘yan ta’addan dake tsaunikan Degbewa da Chinene dukkan su a Mandara.
Ya kara da cewa kafin dakarun sojin saman su kai harin sai da suka gudanar bincike gami da sintiri a yankunan na tsahon kwanaki, wanda ya hadar da tantance adadin ‘yan ta’addan dake rayuwa a wurin.
Ya kuma ce ana zargin wajen matsayin wani wuri na hada abubuwan fashe da killace su.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 18 hours 25 minutes 7 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 20 hours 6 minutes 32 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com