Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci dakarun sojoji da kada su bari ’yan ta’adda su ga bayan al’ummar Nijeriya.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a wani bangare na bikin da rundunar sojin ta gudanar a barikin sojoji na uku da ke Rukuba a Karamar Hukumar Bassa a jihar Filato.
Read Also:
Tinubu wanda ya sami wakilcin Ministan Tsaro, Alhaji Badaru Abubakar, ya ce wajibi dakarun su kare rayukan ’yan kasar a gidaje ko kuma a wuraren mu’amalarsu na yau da kullum.
da yake bayani tun da farko, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya ce sojojin kasar nan kwararru ne tsahon shekaru 161.
Nijeriya dai na fama da matsalolin rashin tsaro wacce ta addabi Arewacin kasar, yayin da na kudanci ke fama da matsaloli barayin mai da masu kokarin ficewa daga ƙasar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 43 minutes 28 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 24 minutes 53 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com