Kungiyar Lauyoyin Nijeriya ta NBA ta ce a cikin yarjejeniyar Samoa babu wani abu da ya tilastawa Najeriya amincewa da ‘yancin ‘yan Madigo, Luwadi, Bisexual, Transgender da Queer (LGBTQ).
Shugaban kungiyar Mista Yakubu Maikyau (SAN), ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yadda labaran Kungiyar NBA na kasa, Mista Habeeb Lawal, Maikyau ya yi gargadi game da munanan labaran da ke tasowa daga bayanan karya kan yarjejeniyar.
Read Also:
“Wannan babu wani tanadi a cikin yarjejeniyar Samoa da ta bukaci Najeriya ta amince ko ta kowace hanya ta amince da LGBTQ ko ‘yan luwadi, ko dai a matsayin wani sharadi na bashi dala biliyan 150 ko kwata-kwata.
PRNigeria Hausa