Gwamnatin Nijeriya ta cire harajin da dukkannin wasu kunji-kunji kan kayan kayan abincin da zaá shigo da su kasar.
wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da ministan noma da samar da wadataccen abinci Abubakar Kyari ya sanyawa hannun a ranar litinin.
abincin da sanarwar ta lisafta sun hadar da samfarerar shinkafa, masara, alkama da kuma tsabar wake.
yace dakatar da biyan harajin na matsayin wani mataki cikin matakan da gwamnati zata dauka nan da kanaki 180 masu zuwa na kawar da matsalar tsadar abinci a kasar.
Read Also:
Ya ce shugaba Tinubu ya amince da janye kudin fito kan muhimman kayan abincin ne har tsawon kwanaki 150, domin saukaka tsadar kayayyakin abinci da ake fama da su.
Ministan, ya bayyana irin ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na yaƙi da hauhawar farashin kayan abinci.
Tsada da matsin rayuwa ya ƙaru tun bayan da Shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Gwamnati za ta shigo da alkama da masara daga waje, Sanarwar ta ce baya ga janye ƙuɗin fito ga ’yan kasuwa masu buƙatar shigo da kayan abinci.
Har wa yau, Gwamnatin Tarayya za ta shigo da alkama kimanin tan dubu 250 da masara tan 250 da za ta bai wa kamfanoni jihohi da ke sarrafa su.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 38 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 19 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com