Masarautar Kano ta tabbatar faruwar gobara da ake zargin kunnata aka yi a fadar Sarkin Kano na Malam Muhammadu Sanusi na biyu.
A sanarwar da shugaban ma’aikatan Sarkin Kano, Munnir Sanusi Abbas ya fitar a yammacin wannan rana ya ce wutar ta tashi ne a safiyar Asabar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, wutar wacce bata yi ɓarna mai yawa ba, ana kan binciken abinda ya haifar da ita.
Read Also:
A cewar sanarwar “Fadar na ɗaukar dukkan matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaron fadar dama mutanen dake ciki, kuma tuni aka fara bincike don kaucewa tashin gobarar anan gaba”.
Tun da fari dai wani rahoto da ya fita a yammacin wannan rana ya ambaci rundunar ‘yan sanda jihar da tabbatar da aukuwar gobarar a fadar sarkin dake kofar kudu a gidan na rumfa.
Ko da dai itama rundunar bata ayyana musabban faruwar gobarar ba tace dai tana bincike ne kan abin da ya haddasa ta.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 12 hours 12 minutes 11 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 53 minutes 36 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com