Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi allawadai da yunƙurin kisan tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.
Trump wanda ke yin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Republican, ya tsallake rijiya da baya bayan an harbe shi, yana cikin jawabi a wajen yaƙin neman zaɓe, a Pennsylvania, lamarin da shugaban Najeriyan ya bayyana a matsayin babban tashin hankali.
Read Also:
Tinubu ya bi sahun sauran shugabannin duniya wajen bayyana takaici a kan harin, yana mai cewa irin wannan rikici bashi da mazauni a turbar dimokuraɗiyya.
A saƙon da Tinubu ya wallafa a shafin X yace harin da aka kai wa tsohon shugaban Amurka, Donald Trump babban abin tashin hankali ne kuma ya saɓawa turbar dimokuraɗiyya.
Sannan kuma ya miƙa jajen sa ga tsohon shugaban ƙasar, tare yi masa fatan samun sauki cikin sauri, gami da da mika ta’aziya ga ƴan uwan wanda ya mutu a harin.
Daga bisani Tinubu ya ce Najeriya tana tare da Amurka a wannan yanayi na alhini.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 13 minutes 53 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 55 minutes 18 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com