Babban sefeton ‘yan sandan Nijeriya, Mr Kayode Egbetukun ya bayar da umarnin gaggawa na dakatar da shirin fara yiwa motocin hawa rijista da kuma samun takardar shaidar tsarin bayanan ababen hawa a kasar ta e-CMR.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar na kasa ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar aka raba manema labarai ranar litinin a birnin Abuja.
Adejobi ya bayyana cewa, dagewar ta biyo bayan yunkurin hukumar na bayar da isasshen lokaci ga Al’ummar kasar, tare da wayar musu da kai a kan rijistar.
Read Also:
sanarwar rundunar ‘yan sandan ta ambaci sefeton na cewa jami’an rundunar sun jinkirta tambayar masu tukin takardar ta e-CMR tukunna
wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Sashen dake kula da cigaban alumma na Kungiyar lauyoyi ta kasa ya bayar da wa’adi ga Sufeto Janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun, da ya gaggauta soke umarnin da aka bayar kan rajistar motoci.
Sashen NBA-SPIDEL ya kuma bukaci sanin dalilin da ya sa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayar da takardar shedar CMRIS, inda ta bayyana cewa babu wata doka da ta bai wa ‘yan sanda ikon bayar da irin wannan lasisi ko satifiket ga masu abin hawa biyo bayan rajistar mota a ofisoshin da suka dace.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 37 minutes 20 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 18 minutes 45 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com