Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu a jihar a yammacin talata.
Gwamnan ya sanya hannu kan kudirin bayan majalisar dokokin jihar ta amince da shi ya zama doka.
Read Also:
tun dai a safiyar talata ne Kudurin kirkirar sarakuna masu daraja ta biyu ya tsallake a majalisar dokokin Kano wadda kuma tace jira kawai take Gwamnan ya sanya hannun ya zama doka.
Sabbin Sarakunan da aka ƙirƙira dai sune na Rano, Ƙaraye da kuma Gaya.
A cewar ƙudurin, dukkansu za su kasance ne ƙarƙashin Sarkin Kano, wanda shi kaɗai ne mai daraja ta ɗaya yanzu a jihar.
PRNigeria Hausa