Mahaifiyar fitaccen mawaƙin nan na siyasa, Dauda Kahutu Rarara, wato Hajiya Halima Adamu, ta shaƙi iskar ’yanci bayan ’yan bindigar da suka yi garkuwa da ita sun sako ta.
Mawaƙi Rararan ne ya tabbatar da sakin nata a shafinsa na Instagram, inda ya ce an sako ta ne da sanyin safiyar Laraba.
Ya bayyana godiyarsa ga Allah sannan ya gode wa sauran jama’a kan gudunmawar addu’o’in da suka yi mata bayan faruwar lamarin.
Sai dai bai yi bayani kan ko an biya kudin fansa ba kafin sakin nata ko kuma a’a.
Read Also:
A baya dai, rahotanni sun bayyana cewar masu garkuwar sun buƙaci a ba su Naira miliyan 900 kafin su sake ta.
Tun kusan mako uku da suka gabata ne dai wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka sace Hajiya Halima mai kimanin shekaru 75 a gidanta da ke ƙauyen Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja ta jihar Katsina.
Rarara dai ya yi suna wajen waƙe ’yan siyasa, musamman na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.
A lokuta da dama, ya sha nuna cewa gwamnatin APCn tana iya kokarinta wajen magance matsalar tsaron da ta addabi ƙasar, ciki har da ta ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 9 hours 19 minutes 44 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 11 hours 1 minute 9 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com