Fadar shugaban kasa ta zargi dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar Jam’iyyar Labour Party Peter Obi da yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
Mataimaki na musamman ga shugaban Bola Tinubu kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a shafinsa na x ranar asabar.
Ya ce akwai zargin magoya bayan Peter Obi, da yunkurin tsige shugaban kasa Bola Tinubu a shirin su na gudanar da wata zanga-zanga mako na sama.
To sai dai guda cikin dattijai a jam’iyyar ta Labour Dr. Chike obidigbo, ya bukaci shugaban kasa bola tinubu ya ja wa Bayo Onanuga kunne bisa yunkurin bisa kalaman da zai kai ga tarwatsa kasar nan.
Read Also:
Obidigbo yace abin takaici ne jin irin wadannan kalamai batanci daga bakin mai taimakawa shugaban kasa na musamman akan harkokin sadarwa, wanda zai kai ga hassalawa wand aba tarwatsawa Nijeriya kawai zai yi ba zai saka kasar nan ne cikin mawuyacin hali.
Bayan shekara guda na gwamnatin Shugaba Tinubu tayi, da yawa daga cikin sauye-sauyen tattalin arziki sun haifar da hauhawar farashin kayayyaki, musamman a bangaren da ya shafi abinci.
Da dama daga cikin yan kasar ne ke ci gaba da bayyana damuwa ganin halin matsin tattalin arziki da suka shiga.
Sai dai magoya bayan Shugaban kasar na ganin cewa Bola Tinubu na iya kacin kokarin sa wajen samnarwa yan kasar da ababen more rayuwa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 21 minutes 34 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 2 minutes 59 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com