Gwamnatin jihar Katsina dake arewa maso yammacin Nijeriya na kokarin samar da wata sabuwar dokar kan iddar mata Mai suna “Iddah Period Law”, domin baiwa mata ma’aikatan gwamnati damar zama a gida na tsawon wata hudu da kwana goma idan mazajensu suka rasu.
Shugaban ma’aikatan jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai.
A cewarsa, gabatar da sabuwar dokar ya biyo bayan kudurin da majalisar dokokin jihar ta gabatar, inda ta bukaci gwamnatin jihar ta duba batun wa’adin Iddah wanda hukumar zartaswa ta amince da shi , tare da yin aiki da shawarwarin da majalisar zartaswa ta gabatar.
Read Also:
Ya kara da cewa, tuni aka fitar da wata takarda ga dukkan ma’aikatun Jihar da na Kananan hukumomin domin baiwa mata ma,aikata damar gudanar da iddah a lokacin da bukatar hakan ta taso.
wannan dai na zuwa ne dai dai da Lokacin da Dan Majalisar tarayya na jamiyyar APC daga jihar Niger ya gabatar da wani kudiri makamancin haka na neman ba wa matan da mazansu suka rasu damar tafiya hutu tare da cikakken albashin ma’auratan da suka rasu, inda kudurin ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar.
Iddah ga matan da mazajen su suka mutu na guda cikin sharuddan da addinin muslunci yayiwa mata a yayin gudanar da ruyuwarsu ta yau da kulum muddin dai bukatar hakan ta taso.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 27 minutes 14 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 17 hours 8 minutes 39 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com