Ƙungiyar Shugabannin Matasan Arewacin Najeriya ta janye zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar.
Shugaban Ƙungiyar shuwagabannin Matasan Najeriya Kwamared Murtala Mohammed Gamji ne ya sanar da hakan, ta cikin wani taron manema labarai da suka gudanar yau a Abuja, inda ya ce sun janye ƙudirin nasu ne a sakamakon yadda suka yi zargin sheɗanci ya shigo cikin shirin nasu.
Jaridar GTR ta ruwaito Gamji na cewa sun ɗauki matakin ne biyo bayan yadda suka gano wasu ɓata gari suna shirya wani mummunan abu, ta hanyar fakewa da zanga-zangar domin rikita ƙasar gaba-ɗaya.
A cewar Gamji ” Ni na fara shirya zanga-zangar kuma wasu mutane sun gayyace ni mun zauna dasu, harma suka shaida min so suke ayi zanga-zangar a iya Jihar Kaduna da Jos da kuma Babban birnin tarayya Abuja, saboda haka dole mu janye shirin namu tunda wasu sun fara yunƙurin cimma burinsu ta hanyar yin amfani damu”.
domin haka ya ce suna kira da dukkan wani ɓangare na al’ummar dake yankin arewa da suyi watsi dayin zanga-zangar, su dawo a haɗa kai abi hanyoyin da suka dace domin neman haƙƙin talakawan ƙasar a wurin shugabanni.
Bugu da ƙari ya kuma shawarci Jami’an tsaro da suyi gaggawar kama dukkan waɗanda suka fito zanga-zangar, domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a dukkan sassan Najeriya.
A ƙarshe ya jaddada cewa suna barranta kansu da yadda ake zagin Malamai, dama yunƙurin fakewa da zanga-zangar wajen lalata dukiyar mutane koma ƙona kayan Gwamnati wanda babu abinda zai haifar illa ƙarin wasu matsaloli a faɗin ƙasar.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 6 hours 40 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 8 hours 21 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com