Babban Bankin Najeriya CBN ya sake yin ƙarin kuɗin ruwa daga kashi 26.25 zuwa kashi 26.75 cikin 100.
Hakan na nufin ƙarin rabin kashi ɗaya ne CBN ya yi, duk da ƙasar na fama da hauhawar farashi da tsadar kayan abinci.
Babban Bankin ya sanar da matakin ne a ranar Talata kuma karo na huɗu kenan a jere Babban Bankin ke yin ƙari a bana.
Tun da farko masana sun yi hasashen yin ƙarin a watan Yuni bayan ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki yayin da kuma darajar naira ta faɗi.
sai dai Babban Bankin ya ce yana ɗaukar matakai na daidaita abubuwa nan gaba.
PRNigeria hausa