Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudurin sauya dokar albashi mafi ƙanƙanta bayan shugaban ƙasa ya aika da buƙatar a yau Talata.
Majalisar ta mince da kuɗirin ne da ke neman tabbatar da ƙarin albashi mafi ƙanƙanta daga N30,000 zuwa N70,000 bayan tsallake karatu na biyu da na uku ba tare da ɓata lokaci ba.
A makon da ya gabata ne ƙungiyoyin ƙwadago suka amince da tayin N70,000 bayan tattaunawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
ko da amincewar da kungiyoyin kwadagon suka yi kan mafi karancin albashin maáikatan yazo matayin bazata ga Alúmmar Nijeriya, sakamakon yadda suka taso da kafin suna bukatar kudade masu tarin yawa sai dai daga bisani sun amince da buktar Tinubu
Rahotanni sun ce kudirin da shugaban ya aika wa majalisam ya ƙunshi har da buƙatar neman sauya shekarun ƙarin albashi daga shekara biyar zuwa uku.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 49 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 31 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com