Shuwagabannin kungiyar mata ‘yan Jarida na jihar Kano Sun yi murabus

Shugabar kungiyar mata ‘yan jarida ta kasa NAWOJ reshen jihar Kano, Hajiya Hafsat Sani da wasu jami’an kungiyar uku sun yi murabus daga mukamansu.

Sanarwar murabus din na zuwa ne yaiyn wani taron kungiyar da ya gudana a sakatariyar kungiyar Yan Jarida a ranar Litinin. Hafsat Sani tace sun yi murabus ne sakamakon wani dalili na kashin.

Lokacin da ta ke karin haske kan murabus, sakatariyar kungiyar Elizabeth Yila, ta bayyana cewa su ba zababbu ba ne a kungiyar rikon kwarya a ka ba su zuwa wani lokaci , Wanda su ka ga dacewar a yanzu su sauka su ba wa wasu dama.

Elizabeth ta kara da da cewa a Jagorancin da Suka yi sun gudanar da ayyukan da aka dora musu daidai gwargwado.

Baya ga shugabar kungiyar da sakatariya da Suka yi murabus akwai Kuma mataimakiyar sakatariya , Ruqayya Umar, da ma’ajin kungiyar Shamsiyya Ibrahim.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com