Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki Gwamnatin Tarayya kan ƙoƙarin dakatar da zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a Nijeriya saboda matsin rayuwa a ranar 1 ga watan Agusta.
Zanga-zangar, wadda matasa suka shirya, na da nufin jawo hankali kan ƙaruwar yunwa da wahala da ’yan ƙasa ke fuskanta.
Masu shirya zanga-zangar sun ce za a shafe kwanaki 10 duba da halin matsi da ke ƙara ta’azzara, wanda suka ce akwai buƙatar kulawar gaggawa daga gwamnatin tarayya da na jihohi.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya jaddada cewa ‘yancin yin zanga-zanga yana cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ya buƙaci gwamnati da ta samar da yanayin tsaro da kwanciyar hankali don gudanar da zanga-zangar lumana, saboda ‘yan ƙasa suna da ’yancin gudanar da taro da bayyana ra’ayoyinsu.
Atiku ya soki gwamnati kan ƙoƙarin take waɗannan haƙƙoƙi, inda ya ce wannan ba ba ya cikin doka kuma yana barazana ga dimokuraɗiyya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 18 hours 7 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 48 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com