Home General Zanga- Zanga: Ministocin Nijeriya sun shiga ganawar sirri

Zanga- Zanga: Ministocin Nijeriya sun shiga ganawar sirri

Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume ya shiga ganawa da ministoci a yayin da ake shirin fara zanga-zanga kan tsadar rayuwa a fadin Najeriya.

Ganawar wacce ke gudana cikin sirri ta samu halartar ministoci sama da 40 na gwamnatin shugaba Tinubu.

Wasu daga cikin ministocin da aka hango a wajen ganawar sun hada da: Nyesom Wike na birnin tarayya Abuja da ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar da Zephnia Jisalo da Tahir Mamman da Atiku Bagudu.

Sauran ministocin sun hada da Wale Edun na kudi da ministan yada labarai Mohammed Idris da sauransu.

wannan dai na  zuwa ne bayan, shugaban kasa Tinubu ya roki matasan Najeriya da su dakata daga shiga zanga zangar ta ‘EndBadGovernance’ da aka tsara farawa a wata mai kamawa.

ko da yake wasu wata kungiya da tayi ikirarin shirya zanga zangar tun da fari a Arewacin kasar ta janye yayin da wata kungiya kuma a jihar kano tace zanga – zanga babu fashi

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna Yusuf
X whatsapp