Ƙungiyar masu masana’antu ta Najeriya ta yi gagaɗi ga gwamnatin ƙasar kan ƙoƙarin gurgunta masana’antun cikin gida.
Ƙungiyar ta yi kiran yin taka-tsantsan da masu ruwa da tsaki kan harakar man fetur da kuma hukumomi sakamakon rikicin gwamnatin tarayya da Matatar Dangote.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Babban Daraktan ƙungiyar Ajayi Kabir ya ce hukumomin gwamnati da ke aikin sa-ido yakamata su inganta yanayi mai kyau na kasuwanci da zuba jari comin ci gaban masana’antun cikin gida.
Ya ce babu wata hukuma da ta kamata ta kawo tarnaki ga babbar masana’anta ta cikin gida kamar Matatar Dangote.
Ya ƙara da cewa masu zuba jari na cikin gida a Najeriya kamar Matatar Dangote suna taka rawa sosai wajen bunƙasa tattalin arziki da biyan haraji da samar da ayyukan yi da kuma ci gaba. Don haka a cewarsa ya kamata a ba su goyon bayan da suke buƙata domin ci gaban kasuwancinsu.
PRNigeria Hausa











