Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), ta ce bata janye daga shiga zanga-zangar matsin rayuwar da ake shirin gudanarwa a ƙasar ba.
Read Also:
Ƙungiyar ta sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, inda ta barranta kanta da labarin da ake yaɗawa na cewa ta fasa shiga zanga-zangar.
Sanarwar da Shugaban Ƙungiyar na ƙasa Kwamared Joe Ajaero ya sanyawa hannu ta ƙara da cewa, duk da ba ƙungiyar ce ta shirya zanga-zangar ba amma hakan bazai hana ta shiga ba, saboda halin ƙunci da matsin da talakawan ƙasar suke ciki a sakamakon wasu matakan da gwamnatin ƙasar ta ɗauka.
Adan haka ne ƙungiyar za ta shiga zanga-zangar domin taya al’ummar ƙasar wannan yaƙi, na nema wa kansu sauƙi a cikin mummunan halin da suke ciki.
Haka kuma ta buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zauna da masu shirya zanga-zangar a teburin sulhu, dangane da buƙatun da suke dashi ta yadda za’a magance matsalar ba tare amfani da ƙarfin mulki ba.
A ƙarshe ƙungiyar tayi fatan Gwamnatin tarayya dana jihohi zasu waiwayi koken ‘yan ƙasar, kuma su biya musu dukkan buƙatun su domin gudun faɗawar ƙasar cikin yanayi da ba’a tsammani.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 28 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 41 minutes 53 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com