Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da Rabon kayan aikin Gayya ga kungiyoyin sa Kai daban daban da yawansu ya kai 160 a Kananan hukumomi 8 da ke cikin birni jihar.
Gwamnan ya ce sun zabi bayar da kayan aikin ne a cikin Kananan hukumomi na birni saboda irin yadda ambaliyar ruwan tafi tsananta musamman a wannan Lokacin na Damuna.
Read Also:
Abba Kabir Yusuf ya ce la’akari da irin nasarorin da suka samu a bara na farfado da Hukumar kwashe Shara ta jiha da kuma Rahotannin da Suka Samu na cewa JIhar Kano na daya daga cikin jihohin da za su iya samun ambaliyar ruwa ya zama wajibi dawo da martabar masu aikin Gayya a Birnin fa karkara, in fa ya ce za su ci gaba da basu tallafin fa ya Kamata.
Daga bisani gwamnan na Jan hankalin Yan kungiyoyin sa kan da su yi amfani da kayan da aka ba su yadda yakamata domin tallafawa kokarin gwamnati na yashe magudanan ruwa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 44 minutes 9 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 25 minutes 34 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com