Gwamnatin jihar kano ta saka dokar hana fita ta tsawon sa’oin 24, bayan bata – gari sun shiga cikin masu gudanar da zanga zangar lumana a jihar.
Gwamnan jihar Abba Kabir yusuf ne ya bayyana hakan yayin da yake ganaw da anema labarai a fadar gwamnatin jihar a yammacin Alhamis dake matsayin ranar farko ta fara zanga zangar.
Read Also:
Ya ce an saka dokar ne domin a dakile sace-sace da fashe-fashen kayan gwamnati da na al’umma da wasu ɓatagari ke yi a ƙarƙashin zanga-zangar.
Ya ce wasu ‘Yan siyasa ne da ba sa son ci gaban Kano ke daukar nauyin yan daba wadanda su ka fake da zanga-zanga su ka fara kai hare-hare.
Ya kuma umarci jami’an tsaro da su gaggauta fara aiwatar da dokar nan take.
PRNigeria Hausa