An samu hatsaniya a Kaduna tsakanin masu zanga-zangar matsin rayuwa da jami’an ƴansanda bayan da ƴansandan suka yi ƙoƙarin tarwatsa masu zanga-zanga da suka yi ƙoƙarin toshe hanyar zuwa gidan gwamnati.
Ƴansandan sun yi amfani da barkono mai sa hawaye wajen korar masu zanga-zangar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Masu zanga-zangar sun kuma far wa ofishin Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa da kare ƙa’idojin hanya ta jihar.
A safiyar yau Alhamis ne masu zanga-zanga suka fantsama kan titunan Najeriya domin nuna fushi kan matsin rayuwa da buƙatar gwamnati ta ɗauki mataki a kai
PRNigeria Hausa












