Jami’an tsaro sun tarwatsa gungun wasu matasa da ke kokarin fasa shaguna su kwashe kayan jama’a a safiyar Alhamis a Jihar Kano.
Jim kadan da fara zanga-zangar tsadar rayuwa a Kano ne matasan suka yi wa wani kafafen shago dirar mikiya da sunan kwasar ganima.
Read Also:
Amma jami’an tsaro sun dakile yunkurin, sun kuma fatattake su.
Haka zalika a yankin unguwar rimin kebe dake karamar hukumar Ungogo matasan da suka fito tun da sanyin safiya sun fara kone-konen tayoyi, akna tinunan unguwar.
Sai dai jami’an tsaro sun sami nasarar tarwatsa su, kowa yanzu dai matasan na cigaba da fitowa ta ko ina zuwa cikin birnin kano.
PRNigeria Hausa