Gwamnatin jihar Kano ta sassauta dokar hana zirga-zirga a jihar daga ƙarfe 12 na rana zuwa karfe 5 na yammacin yau Juma’a, saboda a baiwa mutane damar halartar Sallar juma’a.
Wata sanarwa da ta fito daga jam’ian gwamnatin jihar Kano ta ce dokar dai zata ci-gaba daga ƙarfe biyar na yammacin wannan rana har zuwa lokacin da al’amura suka daidaita.
An shawarci al’ummar jihar da su kasance a gidajensu daga ƙarfe biyar na yammacin yau Jumu’ar domin bin dokar da gwamnatin jihar ta sanya.
A jiya ne Gwamnatin kano ta sanya dokar hana fita a faɗin jihar, biyo bayan shigar ɓata gari cikin zanga-zangar matsin rayuwar da ake tsaka da gudanarwa a faɗin ƙasar.
PRNigeria Hausa