Kungiyar marubuta ta masu rajin kare hakkin dan’Adam a Najeriya, HURIWA, ta soki ‘yansandan kasar kan yadda suke amfani da karfin da ya wuce kima da kuma makamai a kan masu zanga-zangar da ake yi a Najeriya, wadda ta shiga kwana na uku.
A sanarwara da kungiyar ta fitar ta hannun shugabanta Emmanuel Onwubiko, ta ce yadda ‘yansanda ke tunkarar masu zanga-zangar ta lumana a rana ta uku, ko kadan babu kwarewa da nuna mutuntaka, kuma mugun laifi suke aikatawa.
Kungiyar ta nuna damuwa kan yadda ta ce ‘yansandan sun kama mutane da dama da suka taru a babban filin wasa na kasar da ke Abuja,Moshood Abiola Stadium, domin ci gaba da zanga-zangarsu ta lumana a yau Asabar.
Kungiyar ta yi gargadin cewa mummunan matakin da ‘yansandan ke dauka a kan masu zanga-zangar idan ba a ga illarsa ba yanzu to a nan gaba za a gani, abin da zai biyo baya.
Haka kuma ta ce idan ba a fito da ‘yansandan da suka harbi masu zanga-zanga ba an gurfanar da su gaban shari’a, tare da hukunta su kamar yadda doka ta tanada, lamarin zai iya sake janyo zanga-zangar da aka yi ta neman kawo karshen cin zalin da ‘yansanda ke yi wato #ENDSARS.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 17 minutes 31 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 58 minutes 56 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com