Jami’an ‘yansanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zanga a filin wasa na MKO Abiola da ke birnin Abuja, domin tarwasu.
Masu zanga-zangar – waɗanda adadinsu bai kai yadda suka fito a ‘yan kwanakin bayan nan ba – sun taru a filin wasan domin ci gaba da gudanar da zanga-zangar.
Wasu matasan ƙasar ne dai suka shirya zanga-zangar da suka ce ta kwana 10 ne da nufin nuna adawa da matsin rayuwa da ake ciki.
To sai dai bayanai sun ce sa’o’i bayan fara zanga-zangar tasu sai ‘yansanda suka fara harba musu tiyagas da nufin tarwatsa su.
Hukumomin birnin Abuja ne dai suka ware filin wasan a matsayin wurin da za a gudanar da zanga-zangar, bayan umarnin wata kotu ta hana masu zanga-zangar zuwa wasu sassan birnin.
Ko a ranar Juma’a ma ‘yansandan sun harba wa masu zanga-zangar hayaƙi mai sa hawaye a shataletalen Berger da ke tsakiyar Abuja.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 22 hours 36 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1469 days 17 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com