Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a babban birnin jihar da kuma Zariya.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne “bayan nazarin yanayin tsaro a jihar sakamakon tarzomar da aka samu” biyo bayan zanga-zangar da ake yi a sassan Najeriya saboda kuncin rayuwa.
Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta hannun kwamishina mai lura da harkokin tsaro a jihar, Samuel Aruwan ta ce “akwai ƙwararan hujjoji da ke nuna cewa ɓata gari sun ƙwace zanga-zangar, waɗanda suka koma satar kaya da ɓarnata dukiyar gwamnati.”
Gwamnatin ta shawarci al’ummar jihar da su kiyaye da doka da kuma kasancewa a cikin gida, a yayin da jami’an tsaro kuma za su ci gaba da aiki don tabbatar da tsaron lafiyar al’umma.
Jihar kaduna, ta zamo ta baya-bayannan da aka sanya dokar hana fita saboda yadda zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tarzoma.
Kaduna na daga cikin jihohin da aka sanar cewa an samu asarar rayuka tun bayan ɓarkewar zanga-zangar a ranar Alhamis.
An sanya irin wannan dokar a jihohin Kano da Jigawa da Borno da Yobe da Katsina da kuma Filato.
Kodayake, an dage dokar a wasu jihohin, yayin da a wasu kuma aka sassauta dokar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 58 minutes 52 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 40 minutes 17 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com