Home Labarai WAI ta zargi ‘yan sanda da amfani da karfin daya wuce kima...

WAI ta zargi ‘yan sanda da amfani da karfin daya wuce kima akan masu Zanga-Zanga

Kungiyar War Against Injustice tayi Allah wadai da  kasha mutane a wasu unguwannin jihar Kano, yawan wata arangama da dakarun tsaro a lokacin zanga-zanagr tsadar rayuwa a jihar.

Shugaban kungiyar Kwamared Umar Ibrahim Umar, ne ya bayyana hakan inda yace an hallaka mutane  unguwannin na Kurna, Rijiyar Lemo, da Sharaɗa a jihar, da wasu sassan Najeriya.

Muna kira ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta binciki wadannan zarge-zarge tare da daukar matakin da ya dace kan masu aikata laifin.

Haka kuma muna kira ga masu ruwa da tsaki da su ba mu hadin kai wajen neman adalci ga wadanda abin ya shafa da iyalansu. Muna neman a ba da cikakken bayani kan rayukan da aka rasa da kuma jikkatar da aka samu a lokacin zanga-zangar.

Yin amfani da karfi kan masu zanga-zangar lumana cin zarafi ne da take hakkin bil’adama da ‘yancin walwala. Za mu ci gaba da bayar da shawarwarin kare wadannan hakkoki tare da neman a gurfanar da wadanda ke da hannu a wannan ta’asa.

Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna Yusuf
X whatsapp