Ministan kudi da tattalin arziki na Najeriya Mista Wale Edun, ya ce kasar na kashe dimbin kudin da ya kai dala miliyan 600, kwakwankwacin sama da naira biliyan 956.370 a duk wata wajen siyo mai daga waje saboda makwabtan kasashe na cin moriyar man na Najeriya.
Mista Edun ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na AIT, inda ya ce wannan shi ne ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye tallafin mai, saboda Najeriya ba ta san ainahin adadin man da take amfani da shi ba a cikin gida.
Ministan ya ce kasashen da ke amfani da man da Najeriyar ke siyowa daga waje ba wai makwabtanta ba ne na kusa har ma zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wato Santara Afirka.
Ya ce, ”ba Najeriya kadai muke sayo wa ba, muna saya wa kasashe ta gabas, har zuwa Afirka ta Tsakiya. Muna saya wa kasashe na arewa, muna saya wa kasashe na yamma.
Saboda haka dole ne mu tsaya mu tambayi kanmu, har zuwa yaushe za mu ci gaba da yin haka, to wannan shi ne muhimmin abu da ya shafi tattalin arzikinmu.”
Ministan ya ce wannan shi ya sa dole Najeriya ta dauki tsattsauran mtaki kan matsalar saboda tana hana bunkasar tattalin arzikin kasar.
Hukumar kididdiga ta kasar ta ce, yawan man da kasar ke shigowa da shi daga waje ya ragu zuwa kusan lita biliyan daya a wata bayan da Tinubu ya cire tallafin man, ranar 29 ga watan Mayu na bara.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 9 hours 55 minutes 30 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 11 hours 36 minutes 55 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com