Shettima ya magantu kan halin da Nijeriya ke ciki

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya bayyana cewa shugaban kasar na da aniyar ganin ya tallafa wa al’ummar arewacin kasar, sai dai akwai mutanen da ke kawo cikas.

Shettima ya fadi hakan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa a ranar Alhamis. inda ya ce shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu na sane da halin da al’umma ke ciki, kuma yana tausaya masu, “Insha Allah gwamnati na kawo tsare-tsaren ganin cewa la’ummarmu an ɗauki matakin ƙarfafasu.”

Mataimakin shugaban Najeriyar, ya ce sun ɗauki matakai da suka haɗa da cire ton 42,000 na hatsi domin tallafa wa al’ummar ƙasar da kuma ƙarin mafi ƙarancin albashi daga 30,000 zuwa 70,000.

“Bugu da ƙari, akwai gidauniyar taimaka wa ɓangaren noma, inda aka ware biliyon 100 domin a tallafa wa manoma, miliyan biyar, yanzu haka an fara tallafawa, kamar a Jigawa mun noma alkama kusan hekta dubu 65,000, kuma za a yi noman rani daga watan Nuwamba,” In ji Shettima.

Kashim Shettima ya ce gwamnatinsu na ƙoƙarin ganin ta samar da zaman lafiya a sassan ƙasar, musamman a Arewa maso Yamma,inda ya ce ansamu sauƙin matsalar tsaro a wasu jihohin arewacin ƙasar, ” An ɗan samu sauƙi a Borno da Yobe.”

Mataimakin shugaban kasar, Sanata Kashim Shettima ya yi zargin cewa waɗansu ƴan siyasa ne suka yi amfani da zanga-zangar matsin rayuwa da ake ci gaba da yi a ƙasar domin haifar da ruɗani.

“Akwai damuwa a ƙasar, amman gaskiya abun zanga-zangar akwai waɗanda suka shigo,don akwai manufarsu a ɓoye, akwai ƴan siyasa da suke da ɓoyayyar manufa, wanɗanda suke so su kawo ruɗani a ƙasar, suna so su jefa ƙasar a cikin rikicin da ba zamu fita a ciki ba.”

Shettima ya ce suna nan kan bakansu na taimaka wa al’ummarsu domin sun san suna cikin tsananin rayuwa, sai dai ya ce akwai kuma haƙƙin al’umma dake kan hukumomi na kiyaye dukiyoyin al’umma da rayukansu.

Kashim ya yi watsi da zargin da wasu ƴan ƙasar ke yi wa gwamnatinsu na nuna ɓangarenci musamman wajen rabon muƙamai,inda ya ce hakan siyasa ce kawai ” Ministoci 46 ne amman 24 daga arewa ne, manyan shugabannin ma’aikatun gwamnati waɗanda suke da amfani ga arewa, kamar fannin tsaro, da fannin ilimi da noma dukkansu daga ɓangaren arewacin ƙasar suke.”

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce shugaban ƙasar na fifita arewa idan aka yi la’akari da sabuwar hukumar kula da dabbobi da shugaban ƙasar ya samar saboda ƴan arewa su amfana ne.

Shettima ya ce a wajen kasafin kuɗin ƙasar Tinubu ya ba da kaso mai tsoka ga ɓangaren tsaro da ilimi da lafiya. Ya kuma ce suna kan bakansu na shirin samar da matsugunni ga al’ummar da rikici ya raba da muhallansu a arewacin ƙasar.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 18 hours 31 minutes 17 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 20 hours 12 minutes 42 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com