Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar kaduna SEMA ta gargadi wasu kananan hukumomin jihar kan afkawa matsalar ambariyar ruwa, musamman wadanda ke zauna a hanyoyin ruwa.
Babban sakataren hukumar na jihar Dr Usman Mazudu ne ya bayara da gargadin ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu aka raba manema labarai a jihar.
Read Also:
Yace ya zama wajibi a yiwa al’umma kananan hukumomin gargadim duba da yadda aka maka mamakon ruwan sama tsakanin ranakun lahadi da kuma litinin haka kuma ruwan ya cigaba da zuba kakkautawa.
Ya cigaba da cewa mamakon ruwan saman ka iya haifar da tunbatsar koguna, musamman a kananan hukumomin da kogunan ko kuma wadanda kogin ya ratsa ta cikin su.
PRNigeria hausa