Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta raba hatsi tan 1,528.2 a jihar jigawa dake Arewa Maso yammacin kasar.
Wannan na cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin ta na X a ranar litinin, wanda tace rabon kayan na wani bangare na raba kayan abinci ga mabukata a jihohin kasar 36 da birnin tarayya Abuja wanda ya sami shalewar shugaban kasa Bola Tinubu, wanda ke samun kulawara hukumar Noma da samar da abinci ta kasar.
Read Also:
Sanarwar tace wannan hatsina na daga cikin tan dubu 42 da aka fitar daga cikin rumbun gwamnatin tarayya na “National Strategic Reserve”.
Idan za’a iya tunawa a watan Fabreru Gwamnatin tarayyar Nijiriya tace zata raba hatsi tan dubu 42 domin magance tsadar kayan masarufi da al’ummar kasa suke fama da shi a kasar.
Sai dai a watan Maris, an sami rahoton isar hatsin zuwa wasu jihohi da suka hadar da Kano, Kwara, Kogi, Ebonyi, Adamawa, Kebbi, Sokoto, da jihar Taraba.