Fadar Shugaban Najeriya Bola Tinubu ta bayyana cewa shugaban zai yi tafiya zuwa ƙasar Faransa a yau Litinin.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Ba a fayyace makasudin ziyarar ba, amma ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya bayan wani dan lokaci kadan.
Ziyarar ta biyo bayan wata ziyarar da shugaban ƙasar ya kai a kasar Equatorial Guinea a baya-bayan nan, inda ya gana da shugaban ƙasar Teodoro Mbasogo, tare da sanya hannu kan yarjejeniyoyin da suka shafi man fetur da iskar gas, da kuma tsaro.