NLC na tattaunawa kan gayyatar da ‘yan sandan suka yiwa Ajaero

Manyan jagororin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC da suka hada da shugabanta, Joe Ajaero, sun hallara a hedikwatar ƙungiyar ta NLC domin gudanar da wani taron gaggawa na shugabannin ƙungiyar.

Taron ya biyo bayan sammacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi wa Ajaero na ya gurfana a gabanta domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da suka shafi samar da kuɗaɗe ga ayyukan ta’addanci, da cin amanar kasa, da kuma aikata laifuka ta shafukan intanet.

Umarnin ‘yan sanda dai ya buƙaci Ajaero ya gabatar da kansa da misalin karfe 10:00 na safiyar yau Talata domin amsa tambayoyi.

A ranar Litinin ne aka gayyaci Ajaero ta hanyar wata wasiƙa mai dauke da sa hannun ACP Adamu Muazu a madadin mataimakin kwamishinan ƴansanda mai kula da ɓangaren tattara bayanan sirri.

ko dai a makwannin da suka gabata dakarun ‘yan sandan sun kutsa kai ofishin kungiyar dake birnin tarayya Abuja, inda kungiyar ta yi zargin sun yi mata barna a wajen adana litattafan ta gami da tilastawa masu gadi sai sun basu mukullan ofisoshin dake hawa na biyu na ginin.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 38 minutes 51 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 20 minutes 16 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com