Home Labarai Amnesty International ta magantu kan dambarwar NLC da Gwamnatin Nijeriya

Amnesty International ta magantu kan dambarwar NLC da Gwamnatin Nijeriya

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International a Najeriya ta nuna damuwa kan sabbin zarge-zargen taimaka wa ta’addanci da hukumomin kasar ke yi kan ƙungiyar ƙwadago ta NLC da shugabanninta.

A cikin wata takardar sanarwa da ta fitar, Amnesty ta soki yunkurin hukumomin gwamnati da cewa matakin da rundunar ƴansandan Najeriya ta ɗauka na gayyatar Joe Ajaero wani yunƙuri ne kawai na tursasa wa NLC ta yi abin da gwamnati ke so.

A ranar Talata ne wata sanarwa da rundunar ƴansanda ta Najeriya ta fitar ta buƙaci shugaban na NLC, Joe Ajaero ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan wasu tuhume-tuhume da ake masa da suka shafi tallafa wa yunƙurin tayar da rikici a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai a hedikwatar ƙungiyar ta NLC, inda suka ce sun yi hakan ne a wani ɓangare na binciken da suke gudanarwa kan wani mai shirya tarzoma.

Amnesty International ta buƙaci hukumomin da su mutunta ƴancin ƙungiyoyin ƙwadago domin bayyana ra’ayoyinsu, ya kuma yi gargaɗin a guji amfani da ikon gwamnati wajen rufe bakin kungiyar ta NLC.

Amnesty International ta bayyana yadda ake samun karuwar cin zarafin ƙungiyar ƙwadagon a cikin shekarar da ta gabata, ciki har da harin da ƴansanda suka kai wa Ajaero a watan Nuwamba da wani samame da aka kai hedikwatar ta NLC a baya-bayan nan.

Kungiyar ta yi Allah-wadai da waɗannan ayyuka a matsayin katsalandan ga ƴancin kai na ƙungiyar ƙwadagon.

Amnesty ta kuma yi kira da a gaggauta kawo ƙarshen neman murƙushe shugabannin ƙungiyar ta NLC, tare da bayyana zargin da ake yi musu a matsayin maras tushe.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Ƴancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a Bayyane
X whatsapp