Babban mai shari’a na ƙasa na 22, Olukayode Ariwoola ya yi ritaya a matsayin Alkalan Alkalan Nijeriya bayan cika shekarun aiki na shekara 70.
Ariwoola, wanda aka haife shi a ranar 22 ga watan Agusta a 1954, ritayar tasa ta kawo karshen aikin da ya shafe shekaru yana yi a fannin shari’a.
Read Also:
A ranar 22 ga watan Nuwamba na 2011 ne aka nada mai shari’a Ariwoola a matsayin alkalin kotun koli , sannan ya sama babban mai shari’a na Nijeriya a 27 ga watan Yuni na 2022 bayan ajiye aikin da mai shari’a Tanko Muhammad yayi.
A ranar 21 ga watan Satumba na 2022, majalisar dattawa ta tabbatar da shi a matsayin babban alkalin Nijeriya.
Anasa rai dai, Kudirat Kekere-Ekun ce za ta gaje shi bayan majalisar shari’a ta kasa NJC, ta bada shawarar nada ta a mukamin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 10 hours 7 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 11 hours 48 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com