Kungiyar IMN ta ce an kashe mata mutane a Abuja

Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta ce ta kama mabiya mazhabar shi’a da dama, bayan kisan jami’anta biyu yayin wata arangama a Abuja, babban birnin kasar.

Lamarin ya faru ne, lokacin da ‘yan shi’ar ke tattakin yaumul arba’in, da suke gudanarwa kowacce shekara.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Najeriya a birnin Abuja, SP josephine Ade ta ce jamianta na tsaka da aikinsu a wani wurin bincike da ke kusa da kasuwar Wuse ‘yan kungiyar ta IMN suka far musu.

‘’Yaran mu su na aiki, sai ga shi sun fito, mata a gaba da yara, mazan na ta baya, kawai kafin a ankara mai yake faruwa su ka fara jifa da bam din da suka yi da kwalba’’

‘’Ba abinda mu ka yi musu, kawai suka fara kai wa jami’an mu hari, suka kashemu na ‘yansanda guda biyu tare da raunata wasu uku sannan sun kona motocci guda uku’’ in ji ta

Rundunar ‘yansanda Najeriya ta ce su na kan gudanar bincike akan abinda ya haifar da yamutsin :

‘’Mun kama wasu ‘yan shi’a a lokacin kuma muna kan bincike domin mu san abinda ya haifar da yamutsin. Ba bu wani da aka kashe daga bangaren ‘yan shi’ar’’ in ji ta

Sai dai daya daga cikin jagororin kungiyar ta IMN Malam Abdullahi Muhammad Musa ya ce ba haka abin ya wakana ba.

Ya ce tun ranar jamu’a suka fitar da sanarwar a kan cewa za su fito su yi tattaki kamar yadda suka saba duk shekara:

“Lafiya lau muka zo Wuse 2, mu na zuwa kasuwar Wuse ‘yansanda su ka bude ma na wuta, wasu su ka yi gaba da tattakin, har mu ka je Berger su ma ‘yansandan da ke Berger su ka harba ma na hayaki mai sa hawaye, sun harbi mutane da dama, a gaba na wani ya mutu’’

Ya yi ikirarin cewa ‘yan sandan sun harbi mutane da dama tare da musanta zargin cewa suna rike da makamai kuma sun tare wuri

“Ba mu taba tare wa kowa hanya ba , Su dai kawai sun bude ma na wuta , ba yau su ka saba kashe mana mutane ba’’ in ji shi.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 9 hours 51 minutes 56 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 11 hours 33 minutes 21 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com