• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home General Cutar diphtheria ta kashe mutane 40 bayan sake ɓulla a Kano
  • General
  • Labarai

Cutar diphtheria ta kashe mutane 40 bayan sake ɓulla a Kano

By
Diphtheria, Kano
-
August 29, 2024
Arewa Award

Sabuwar annobar cutar mashaƙon diphtheria da ta ɓarke a jihar Kano ta arewacin Najeriya ta laƙume rayukan fiye da mutane 40 yayinda wasu gommai yanzu haka ke kwance a asibitoci don karɓar kulawa bayan harbuwa da cutar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wakilinta ya ganewa idonsa cikar asibitin kula da cutuka masu yaɗuwa na jihar Kano da ake kira IDH ko kuma ‘zana’ maƙil da waɗanda suka harbu da cutar.

Wani jami’in asibitin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar mata da yawaitar mutuwar da ake gani kullu yaumin sanadiyyar cutar a cikin nasibitin na Zana ko kuma IDH.

Bayanai sun ce har zuwa tsakar ranar jiya anga dandazon marasa lafiyar da ke son ganin likita a asibitin na Zana sakamakon alamomin cutar ta mashaƙon diphtheria.

Read Also:

  • Bama goyan bayan ayyukan ta’addanci a Najeriya – Miyetti Allah
  • Sojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a Katsina
  • Shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kai

Rahotanni sun ce makwanni biyu kenan a jere ana ganin ƙaruwar masu fama da wannan cuta da kan riƙe maƙogwaro tare da haddasa zazzabi da kuma ƙuraje a baki ko ɗaɗewar harshe da sauyawar kalar ido.

Wasu majiyoyi sun ce rashin kayakin aiki dama ƙwararrun likitocin da ke duba wannan cuta a sassan jihar shi ne ya haddasa cunkoson jama’a a asibitin wanda ke tsakar birnin Kano.

Tuni dai masu ruwa da tsaki suka ɗaura ɗamarar fara aikin wayar da kan jama’a game da alamomin cutar da kuma yadda za a baiwa kai kariya daga harbuwa da ita, lura da kasancewar cutar ta diphtheria a sahun cutukan da wani kan gogawa wani.

Alƙaluma sun nuna cewa wannan cuta ta fi illa ga ƙananan yara ta yadda ta ke farowa kamar mura gabanin tsananta tare da haddasa asarar rayuka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Previous articleShugaban NLC ya kammala ganawa da ƴansanda kan zargin ta’addanci
Next articleSojoji sun hallaka ‘Yan Ta’adda 8 a jihar Kaduna
Diphtheria, Kano

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Bama goyan bayan ayyukan ta’addanci a Najeriya – Miyetti Allah

Sojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a Katsina

Shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kai

Gwamnonin PDP na taro a Zamfara

Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai – Musa

Hukumar KAROTA ta kaddamar da kotun tafi da gidanka a jihar Kano

kotu ta dakatar da asusun banki huɗu na Mele Kyari

Ana neman mutane 40 a cikin Kogi bayan kifewar kwale-kwale a Sokoto

A biya mu haƙƙoƙinmu, ba mu son bashin gwamnati – ASUU

Amurka za ta sayar wa Nijeriya makamai da kuɗinsu ya kai dala miliyan 346

PDP za ta ƙaddamar da kwamitocin zartaswa na shiyoyi

EFCC ta ba da belin tsohon gwamnan Sokoto Tambuwal da ta tsare

Recent Posts

  • Bama goyan bayan ayyukan ta’addanci a Najeriya – Miyetti Allah
  • Sojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a Katsina
  • Shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kai
  • Gwamnonin PDP na taro a Zamfara
  • Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai – Musa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1529 days 11 hours 40 minutes 26 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1511 days 13 hours 21 minutes 51 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
Bama goyan bayan ayyukan ta'addanci a Najeriya - Miyetti AllahSojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a KatsinaShalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kaiGwamnonin PDP na taro a ZamfaraYa kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai - MusaHukumar KAROTA ta kaddamar da kotun tafi da gidanka a jihar Kanokotu ta dakatar da asusun banki huɗu na Mele KyariAna neman mutane 40 a cikin Kogi bayan kifewar kwale-kwale a SokotoA biya mu haƙƙoƙinmu, ba mu son bashin gwamnati - ASUUAmurka za ta sayar wa Nijeriya makamai da kuɗinsu ya kai dala miliyan 346PDP za ta ƙaddamar da kwamitocin zartaswa na shiyoyiEFCC ta ba da belin tsohon gwamnan Sokoto Tambuwal da ta tsareMajalisar Dokokin Kano ta Dakatar da Ciyaman din RanoƘananan dillalan mai sun zargi shugabanninsu da yiwa Matatar Dangote zagon ƙasaAtiku Abubakar ya magantu kan tsare Tambuwal da EFCC ta yi
X whatsapp