Kamfanin mai na kasa NNPC ya ce yana neman kamfanunuwa masu zaman kansu da za su iya ci gaba da rike matatar mai ta Warri da ta Kaduna.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.
Matatar mai ta Warri wacce ke jihar Delta, an kaddamar da ita ne a shekarar 1978 da manufar samar da tattacen mai ga kasuwannin kudu maso yamma da kudancin Nijeriya.
Read Also:
Itama matatar mai ta Kaduna, an kafata ne a shekarar 1980 domin samar da tataccen man fetur ga Arewacin Nijeriya
Sai dai matatun sun shafe tsawon lokaci basa aiki.
tun bayan dai fara aikin matata man fetur ta Dangote aka shiga sa toka sa katsi tsakanin kamfanin Man na NNPC da sabon kamfanin na Dangote da ake kallon zai kawo karshem tsalolin man fetur da ake fama da shi a kasar shekaru da dama.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 14 minutes 57 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 56 minutes 22 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com