Shugaban kungiyar dake rajin kare hakkin Dan Adam da wayar da kai (CHRICED) Dakta Ibrahim M Zikirullahi ya bayyana cewa, Jahar Kano na kokari wajen tabbatar da an samu Cigaba mai dorewa a fannin lafiya ta bangare Samar da doka akan rage mace mace mata Masu juna biyu da kananan yara tun lokacin Tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso a shekarar 2001.
Dakta Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai da kuma kungiyoyi Masu zaman kan su kan Samar da hanyoyin magance matsalar yawan mace-mace mata Masu juna biyu da kananan yara ta Samar da dabaru don zantar da dokar haihuwa kyauta.
Read Also:
Kididiga na nuna cewa, jihar Kano na Cigaba da zama a sahu farko wajen samun yawan Mace -mace mata Masu juna biyu da kananan yara a kasar, Wanda haka ya zama barazana ga fannin lafiya a kasa.
Dakta Ibrahim ya Kara da cewa, rashin zartar da dokar haihuwa kyauta a asibitocin mu na Kara yawan mace-mace mata Masu juna biyu da kananan yara.
Hakazalika, zartar da dokar zai Kara bawa kananon asibitocin da ke a matakin farko Samar Samu kulawa tare da horar da likitoci da kuma Kara inganci aikin su .
Tabbas Gwamnoni da ake yi a Kano sunyi kokari wajen Samar da Dokar Wanda har yanzu wasu jahohin na matakin farko,sai dai zartar da dokar a jahar na zama tsaiko idan ka ga yadda kididiga ke nuna wa tun bayan kaddamar da dokar a watan mayu shekarar 2023.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 37 minutes 24 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 18 minutes 49 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com