Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Nijeriya tayi Allah wadai tareda nuna rashin Jin dadinta bisa tashin gwauron zabi da man fetur yayi a fadin Kasar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kungiyar ta fitar bayan da kamfanin Man Fitor na kasar NNPCL ya fitar da sanarwar Kara farashin Man fetur.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar da Sakataren Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa Shehu Tasiu Ishaq da sakataren yada labarai na Kungiyar Abubakar Balarabe Kofar Naisa suka sanyawa hannu tace bisa la’akari da halin da ‘Yan kasa ke ciki akwai bukatar a duba lamarin.
Kungiyar ta bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rage farashin Man fetur din a maimakon Kara farashin sa, domin saukakawa al’ummar Nijeriya.
Daga bisani sanarwar ta bukaci al’ummar kasar su cigaba da yin addu’oi na neman samun sassaucin al’amura da samun cikakken tsaro da wadatar arziki a Kasa baki daya.
PRNigeria Hausa











