Gwamnatin Jihar Kano ta saka ranar 16 ga watan Satumba domin komawa makarantar Firamare da Sakandire na zangon farko na shekarar 2024/2025 ga dukkan makarantun kwana da na firamare masu zaman kansu dake jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu aka raba ta ga manema labarai a jihar, wadda ta ce ta iyaye da wakilansu su lura da sabuwar ranar da za su ci gaba da aiki domin tabbatar da bin doka.
Read Also:
sanarwar ta ce Makarantun kwana a fadin jihar za su koma ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024.
Idan dai ba a manta ba, kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya sanar a ranar Asabar 7 ga watan Satumba, dage ranar da za a koma makaranta.
Sanarwar ta sake jaddada kudurin gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusif na ganin kowane yaro ya samu ilimi mai inganci.
“Gwamnati na daukar matakai masu kyau wajen samar da ingantaccen yanayin koyo da zai zaburarwa da karfafawa dalibanmu kwarin gwiwa a fannin ilimi,” in ji sanarwar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 34 minutes 37 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 16 minutes 2 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com