Mahukuntan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun tiso keyar ƴan Najeriya 400 sakamakon zama a ƙasar ta yankin gabas ta tsakiya ba bisa ka’ida ba, matakin da ke zuwa makwanni bayan dawo da bayar da biza da ƙasar ta yi ga al’ummar Najeriyar.
Rahotanni sun ce manyan hukumomin ƙasar da suka haɗa da na agaji da mai kula da ƴan cirani da masu kula da shige da fice da kuma hukumar yaƙi da safarar mutane baya ga jami’an ofishin babban mai bayar da shawara kan sha’anin tsaro na Najeriyar ne suka tarbi mutanen a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja fadar gwamnatin ƙasar.
Read Also:
Kamar yadda aka ruwaito, mutanen 400 sun ƙunshi mata 90 da kuma maza 310 waɗanda bayanai suka ce wasunsu izinin zamansu a ƙasar ta Haɗaɗɗiyar daular Larabawa ya ƙare amma suka ƙi ficewa yayinda wasunsu suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.
Galibi ƴan Najeriyar kan yi amfani da damar shiga ƙasar da nufin karatu ko kuma cinikayya amma sai su juye zuwa ƙwadago ba tare da takardun izinin yin aiki ba.
Haka zalika akwai bayanan da ke alaƙanta ƴan Najeriyar da aikata ba dai dai ba a ƙasashen musamman na gabas ta tsakiya lamarin da a lokuta da dama kan kaiwa ga korosu gida.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ƙasashe ke tiso ƙeyar ƴan Najeriyar ba, domin kuwa ko a Juma’ar da ta gabata sai da Turkiya ta kwaso ƴan Najeriyar 103 tare da miƙasu ga hukumar NEMA, yayinda ko a karshen shekarar bara, Saudiya ta tiso ƙeyar ƴan Najeriya 264 zuwa gida bayan da ta soke bizar su jim kaɗan bayan saukarsu a filin jirgin saman Sarki Abdul’aziz da ke birnin Jidda.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 40 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 21 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com