Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin 16 ga watan Satumba, a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar, domin bikin ranar Maulidi.
Cikin wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar cikin gida ta ƙasar, Dr. Magdalene Ajani ya fitar, ya ce ministan ma’aikatar, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hutun a madadin gwamnatin tarayya.
Al’ummar musulmai a faɗin duniya na gudanar da bukukuwan Maulidi domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W)
”Gwamnati na taya al’ummar musulman ciki da waɗanda ke zaune a ƙetare murnar zagayowar ranar Maulidin”, in ji sanarwar.
Haka kuma ministan ya yi kira ga musulman ƙasar su yi amfani da lokacin bukukuwan wajen yi wa ƙasar addu’ar zaman lafiya da ci gaban ƙasar.