Hukumar zabe a Najeriya INEC ta sanar da cewa sama da mutum miliyan biyu ne suka karbi katin zaɓensu na dindindin gabanin zaɓen gwamnan jihar Edo da ke tafe ranar Asabar.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta ce mutum 2,629,025 suka yanki katin zaɓe a faɗin jihar.
“An karɓi katuna 2,249,780 yayin da 379,245 sune suka rage ba a karɓa ba zuwa ranar Litinin 16 ga watan Satumban 2024 bayan ƙara wa’adi da muka yi,” in ji INEC.
Hakan ya nuna cewa an karɓi kashi 85.57 na katunan zaɓe a jihar, a cewar hukumar.
Za a gudanar da zaɓen a ɗaukacin rumfunan zaɓe 4,519 da ke faɗin jihar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 58 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 39 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com