Tababa da rashin tabbas sun mamaye ziyarar hukumar EFCC da tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello yace ya yi domin amsa tambayoyi dangane da zarge zargen da ake masa na rub da ciki da kudaden talakawa da kuma halarta kudaden haramun.
Yayin da tsohon gwamnan ta hannun mai magana da yawunsa Ohiare Michael ya ce yau ya kai kansa EFCC tare da rakiyar lauyoyinsa da kuma gwamnan Kogi Usman Ododo, Hukumar EFCC ta fitar da sanarwar watsi da ikrarin da kuma bayyana cewar har yanzu ta na neman shi ruwa a jallo.
Read Also:
Bello ya shaida wa manema labarai cewar bayan ziyarar domin amsa tambayoyi EFCC ta ce masa ya tafi gida ba tare da masa tambayoyi akan zargin karkata kudaden da suka kai naira biliyan 80 ba.
Tsohon gwamnan ya bukaci hukumar yaki da cin hancin ta ci gaba da aiki da dokokin da suka samar da ita tare da mutunta ‘yancin jama’ar kasa, ya yin da ya kara da cewar matakan da ya dauka na kin amsa gayyatar hukumar ya yi su ne domin kare hakkokinsa.
Sai dai mai magana da yawun EFCCn Dele Oyewale ya ce babu gaskiya dangane da mika wuyar tsohon gwamnan, kuma har yanzu suna neman sa ruwa a jallo.
Ko da yake a safiyar Alhamis, jami’an hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati na EFCC sun zagayi gidan da ake zargin Yahaya Bello na ciki, wanda suke bukatar ya mika kansa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 30 minutes 9 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 17 hours 11 minutes 34 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com