Home AFIRKA ECOWAS ta caccaki hare-haren ta’addanci da aka kai babban birnin Mali

ECOWAS ta caccaki hare-haren ta’addanci da aka kai babban birnin Mali

Ƙungiyar ƙasashen yammmacin nahiyar Afrika,  ECOWAS ta caccaki hare-haren da ƴan ta’adda su ka kai babban birnin Mali, Bamako a ranar Talata.

A wata sanarwa, ECOWAS ta bayyana rashin jin  daɗin ta a game da waɗannan hare-hare, waɗanda ta ce su na barazana ga zamn lafiyar yankin yammacin nahiyar  Afrika.

Sanarwar ta kara da cewa Kungiyar ta na jaddada ƙudirinta a kan duk wani shiri da kawo zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

A ranar Talata ce aka kai wa birnin Bamako munanan hare-hare, waɗanda ƙungiyyar nan mai ikirarin jihadi da ke da alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kaiwa. Har yanzu dai  ba a bayyana adadin mutanen da waɗannan hare-hare su ka rutsa da su ba.

Birnin Bamako bai cika fuskantar hare-hare na masu ikirarin jihadi ba kamar yadda wasu sassan kasarke fuskanta kusan kullayaumin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp