Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya soke Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso, ya mayar da ita kwalejin ilimi.
Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano, Baba Ɗantiye, ya sanar cewa, “Gwamna ya rushe hukumar gudanarwar jami’ar nan take”, ya mayar da ita tsohon matsayinta na Kwalejin Ilimi na Sa’adatu Rimi.
Read Also:
A cewarsa, an gano cewa tun da farko akwai illa a ɗaga darajar Kwalejin Ilimi na Sa’adatu Rimi zuwa jami’a, la’akari da “kasancewarta a mashigar garin Kano inda dalibai da dama daga wajen birnin suke karatu.
“Hakan na haifar da barazanar rasa ƙwarrarrun malamai, bambancin albashi da kuma matsalolin gudanar da ita cikin inganci.
“Sannan Majalisar Zartarwa ta lura cewa jihohi da dama a faɗin Najeriya sun ci gaba da gudanar da kwalejojin iliminsu ba tare da wata matsala ba, ƙarƙashin tsarin bayar da takardun shaidar kwarewar malanta da kuma shaidar digiri, ba tare da kwalejojin sun koma jami’o’i ba.”
A cewarsa, soke matsayin jami’ar “ba zai shafi karatun ɗalibanta ba, kuma kwalejin za ta kasance mai bayar da shaidar kammala karatun digiri.
“Sannan za ta ci gaba da gudanar da darussa a wasu fannonin,” da ba na ilimi ba.
Ana iya tuna cewa tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ce ta daga darajar kwalejin ilimin na Sa’adatu Rimi mallakar gwamnatin jihar zuwa jami’ar ilmi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 17 hours 4 minutes 42 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 46 minutes 7 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com