Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar Edo ta yi kira ga hukumar zaɓen ƙasar da ta bayyana sakamakon zaɓen da ke kan na’urorin adana sakamakon zaɓe na hukumar wato IREV.
Gwamnan jihar Godwin Obaseki da takwarorinsa na jihohin Adamawa da Taraba ne suka bayyana haka a wani taron manema labarai da suka gabatar a ɗakin tattara sakamakon zaɓe na jam’iyyar wato ‘ PDP Situation Room’.
Gwamnonin uku sun zargi hukumar INEC da rubuta sakamakon da ba na gaskiya ba a kan takardar rubuta sakamakon a wasu rumfunan zaɓen jihar.
Tuni dai hukumar zaɓen ta ce ta ƙaddamar da bincike kan zargin rubuta sakamakon bogin a kan takardun rubuta sakamakon zaɓen.
Sannan ta buƙaci a kwantar da hankali da bin doka da oda da mutunta juna yayin da take dab da fara aikin karɓar sakamakon.
to sai dai tuni hukumae ta INEC ta fara barra sakamakon zaben ina a karamar hukumar Esan ta Yamma
APC – 12952
PDP – 11004
sai kuma karamar hukumar Owan ta Yamma
Read Also:
APC – 12277
PDP – 11284
Karamar hukumar Uhunmwode
APC – 8776
PDP – 9339
a karamar hukumar Ovia ta Arewa maso yamma kuwa
APC – 13225
PDP – 15311
sai kuma karamar hukumar Esan ta kudu maso Gabas
APC – 8398
PDP – 14199
haka kuma hukumar ta INEC ta bayyana sakamakon karamar hukumar Egor inda tace
APC – 16760
PDP – 14658
wadannan dai sakamakon manyan Jam’iyyun siyasa a jihar ne wadanda ke kan gaba wajen yawan kuri’a a zaben da ya guda a ranar asabar a jihar ta Edo.
PRnigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 55 minutes 5 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 36 minutes 30 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com